The Soda Pop
Aika + f p _ x
WASU SHAFUKAN NTAHAUSA
HOTONA LABARAI
MusicsVideosForumGames ApplicationsThemes
+Labarai Da Rahotonni

Shin me ku ka sani game da 'yan matan Chibok?

image

Shekaru biyu kenan tunda kungiyar Boko Haram, ta sace yara mata 276 daga wata makaranta a arewa maso gabashin Najeriya.

Sace su da aka yi ya janyo daya daga cikin gangami da aka fi samu a kafofin sada zumunta da muhawara, inda aka kirkiro wani maudu'i mai suna #BringBackOurGirls.

Amma kuma har yanzu ba a ga 'yan matan ba. NTA HAUSA kuma ta duba lamarin kawo yanzu.

An rufe yawancin makarantu a yankin sakamakon hare-hare da Boko Haram ke kai masu, domin akidarsu ta yaki da ilimin Boko,
wanda suke gani shi ke bata tarbiyyar da addinin musulunci ya tanadar.

Ba a taba kai hari garin Chibok ba a baya, saboda haka hukumomi suke ganin makarantar mafaka ce mai kyau ta gudanar da jarabawar kammala sakandare.

'Yan bindigar sun dira ne cikin dare, inda suka shiga dakunan kwanan 'yan matan su 276 suna harbe-harbe, daga bisani suka tattare su cikin motocin akori kura.

Wasu sun yi nasarar kubucewa sa'o'i kadan bayan an yi garkuwa da su, ta hanyar tsallakowa daga cikin motocin akori kurar, suka kuma tsere cikin dazukan da ke kusa.

Baki daya dai mayakan sun sami tafiya da yara 219.

Meye yasa aka sace su?

Daya daga cikin wadanda suka yi nasarar kubucewa ta shaida wa sashen Hausa na NTA abin da mayakan suka ce musu; "Kun zo karuwanci ne kawai a makaranta, saboda karatun Boko haramun ne, don haka me kuke yi?"

A baya dai mayakan sun musanya wadanda suka yi garkuwa da su, da 'yan kungiyar da ke daure a matsayin fursunoni, amma sace
yara matan ya zo gabannin karfi da kungiyar ta kara yi bayan ta kwace iko da wasu yankuna.

Kungiyar ta mayar da mazauna yankuna da suka kwace bayi, kuma suka tirsasawa yara maza da suka tadda shiga kungiyar, mata kuma aka daura masu aure dole da mayakan.

Ina ne karshen ganinsu?

Wani hoton bidiyo da gidan talabijan na CNN ya fitar a watan Afrilun shekarar 2016 ya nuno wasu cikin yaran makarantar a raye.

Bidiyon ya nuno yara mata lullube cikin hijabi su 15, inda suka bayyana cewa ana kula da su, amma suna bukatar komawa ga
iyayensu.

Rahotanni sun ce an dauki hoton bidiyon ne a ranar Kirisimeti, kazalika iyayen wasu cikin yaran da aka nuno sun gane 'ya'yansu.

Yawancin 'yan matan makarantar Chibok din Kiristoci ne, wadanda rabon da a gansu tun watan Mayun shekarar 2014, lokacin da
Boko Haram ta fitar da wani bidiyon wasu 130 daga cikinsu, an tara su suna karatun Al'Qurani.

Lokacin da gwamnatin kasar ta sanar da tsagaita wuta domin a tattauna batun sulhun da zai kai ga sakin yaran ne, jagoran kungiyar ya yi watsi da yarjejeniyar, inda ya ce duk sun musuluntar da yaran kuma sun aurar da su.

A shekarar da ta gabata ne wasu mata uku da a cewarsu an ajiyesu sansani daya da 'yan mata Chibok din suka shaidawa NTA cewa, wasu cikinsu sun zama mayakan
kungiyar, duk da cewar ba a tabbatar da batun ba.

An gano cewa jita-jitar an ga yaran a kasashen da ke makwabtaka da Najeriya babu gaskiya ciki.

Wani dan jarida da aka yi amannar cewa yana da alaka da 'yan Boko Haram, Ahmed Salkida, a watan Disamba ya ce yana da
labarin cewa matan na nan da ransu.

To shin me ake yi domin samo su?

Amurka da Biritaniya da Faransa na bayar da taimakon soji da bayanan sirri domin nemo 'yan matan.

Kasashen China da Isra'ila ma sun bayar da agaji.

An kaddamar da hadakar hadin gwiwar sojoji 8,700, daga kasashen Kamaru da Chadi da Nijar da Najeriya.

Matsa kaimi da aka kara a kwanan baya ya yi nasarar fatattakar mayakan daga birane da kauyuka da a baya suke iko da su, zuwa
maboyarsu a dajin Sambisa, inda ba ya shiguwa ta dadi.

Sojoji sun 'yanta dubban mutane daga hannun Boko Haram, amma har yanzu ba amo ba labarin 'yan matan Chibok.

Share Button

Mungude da karanta Shin me ku ka sani game da 'yan matan Chibok?
An wallafa shi a 2016-04-15 18:54
Alaka Boko Haram , Chibok
Ra'ayuyi Shin me ku ka sani game da 'yan matan Chibok?
Antispam
visitors online visitors today visitors yesterday visitors total