Old school Easter eggs.
Aika + f p _ x
WASU SHAFUKAN NTAHAUSA
HOTONA LABARAI
MusicsVideosForumGames ApplicationsThemes
+Labarai Da Rahotonni

Yawan Alhazan Najeriya da suka mutu zai haure 54

image
Alkaluman da ke kara fita na wadanda suka mutu a turmutsutsun da ya faru a
kasar Saudia na nuni da yiwuwar na Najeriya su haura 54.


Sarkin Kano kuma shugaban mahajjatan Nigeria na bana, ya yi kira da a sake duban batun zaman Mina musamman ga alhazan Nigeria dake shan matsananciyar wahala yayin zuwa jifa.

Har zuwa yanzu akwai alhazan da dama da ba a gansu ba, kana akwai manyan motocin 14 dauke da gawawwaki da ba a kai ga shigar da su dakunan ajiye gawawwaki ba saboda cunkoso.

Babban sakataren hukumar aikin hajji ta Kano Malam Abba Yakubu ya shaidawa NTA cewa kawo yanzu alhazan Kano tara ne aka
tabbatar sun mutu a turmutsutsun, sannan kuma suna ci gaba da bincika asibitoci dan neman wadanda suka bata.

Kasashen Alhazan da suka rasu;

¤ Iran: 169

¤ Morocco: 87

¤ Egypt: 55

¤ Nigeria: 54

¤ Indonesia: 41

¤ India: 35

¤ Cameroon: akalla 20

¤ Niger: 22

¤ Pakistan: 18

¤ Ivory Coast: 14 , 77 sun bace

¤ Chad: 11

¤ Somalia: 8

¤ Algeria: 8

¤ Senegal: 5

¤ Libya: 4

¤ Tanzania: 4

¤ Kenya: 3

¤ Burkina Faso: 1

¤ Burundi: 1

¤ Netherlands: 1

¤ Tunisia: 1

¤ Benin: ba a san adadin ba

Share Button

Mungude da karanta Yawan Alhazan Najeriya da suka mutu zai haure 54
An wallafa shi a 2015-09-28 07:16
Alaka Alhazan , Dasuka. Mutu , Najeriya
Ra'ayuyi Yawan Alhazan Najeriya da suka mutu zai haure 54
No Photo
Yahaya zakariya skf
2016-11-11 13:08

Allah jikansu da rahamah ameen summah améen

No Photo
HARUNA YAHAYA
2015-09-28 08:43

lnnalillahi wa'inna alaihim raji'un

Antispam
visitors online visitors today visitors yesterday visitors total