Lamborghini Huracán LP 610-4 t
Aika + f p _ x
WASU SHAFUKAN NTAHAUSA
HOTONA LABARAI
MusicsVideosForumGames ApplicationsThemes
+Labarai Da Rahotonni

Dubu Dari Biyar Aka Ba Mu Domin Mu Kashe Sheik Sani Yahaya Jingir, Inji Maharan Jos Da Zaria

imageimage
Maharan da suka kitsa Harin Bom a Jos da
Zaria sun ce naira dubu dari biyar aka ba su
domin kashe Shugaban Majalisar Malamai
na Kuniyar Izala na Kasa Sheik Malam Sani
Yahaya Jingir.

Sun bayyana haka ne jim kadan bayan
kama su da Rundunar Sojojin kasar an ta yi
jiya a Gombe.

"Ali yana cikin Dajin Sambisa shine ya ce mu
je mu kashe Yahaya Jingir kuma ya ba mu
kudi Naira Dubu Dari Biyar , amma
Abubakar shine ya san komai a cikinmu
mun je da Bom da kuma bindiga amma mai
bindigar ya mutu" inji daya daga cikin
Maharan.

Shi kuwa direban na su ya ce bai san komai
ba, shi dai an ba shi dubu goma aka ce ya
kai su Jos da Zaria idan suka kammala
abinda za su yi ya dawo da su ya sauke su
a inda ya dauke su, wato kan hanyar shiga
MaiDuguri.

Saidai daya daga cikin maharan ya karyarta
Direban na su, inda ya ce babu abunda bai
sani ba domin tare suke aiwatar da komai
da shi.

Shugaban nasu mai suna Abubukar bai
samu damar furta komai ba kasancewa
Raunin dake Kafarsa dalilin harbin Bindiga
ya hanashi cewa
komai.

Rundunar Sojojin Nijeriya dai sun kama
maharan ne a jiya tare da hadin gwuiwar
jami'an tsaro na farin kaya SSS a garin Deba
karamar Hukumar Yamaltu dake Jihar
Gombe a daidai wani shingen binciken
ababen hawa.

Share Button

Mungude da karanta Dubu Dari Biyar Aka Ba Mu Domin Mu Kashe Sheik Sani Yahaya Jingir, Inji Maharan Jos Da Zaria
An wallafa shi a 2015-07-09 18:14
Alaka Maharan Jos Da Zaria , Sheik Sani Yahaya Jingir
Ra'ayuyi Dubu Dari Biyar Aka Ba Mu Domin Mu Kashe Sheik Sani Yahaya Jingir, Inji Maharan Jos Da Zaria
No Photo
Abdulkadir musa
2015-07-10 02:07

Allah ya karatuna masu asiri.

No Photo
Halluru usman
2015-07-10 00:51

Allah yakarato namusu Asiri

No Photo
AUWALU YUNUS
2015-07-10 00:04

ALLAH KAKARA TONA MUSUASIRI

No Photo
Ishaq Abdullahi
2015-07-09 23:29

Yayi dai dai amma bama ra'ayin wannan shingayen wahalan da mukasha don Allah abarta haka nan ko tsoho be yazo da Babur dai ya sauna ya tura ko Mara lafiya me ga karban kudi kuma da zaran kayi wani kuskure a wulakantaka ko abaka aikin da zaka koma kayi jinya gaskiya mungaji haka. Shi kuma Bihari da yatashesu Allah yaji kan iyayenshi yabasu aljanna amin

No Photo
Nura Mohd
2015-07-09 22:56

Allah ya kiyaye gaba.

No Photo
Hayatuddeen Nuraddeen
2015-07-09 22:37

Allah ubangiji yakara tona asirinsu Ameen.

No Photo
Maude Muhammad UBA BANK
2015-07-09 22:23

Alhamdu lillahi masha Allahu Allah ya chi Gaba Da To Na Asirinsu Aduk Inda suke Amin summa Amin

No Photo
ABDULLAHI A U DALLARE
2015-07-09 22:13

TO AI DAMA RANA DUBU TABARAWO DAYA TAK TAMAIKAYA

No Photo
Haruna mohd birninkudu
2015-07-09 21:39

ALLAH KA TONA ASIRIN DUK WANI WANDA YAKEE DA HANU A CIKIN WANNAN AL'AMARI

No Photo
Yushau samaila
2015-07-09 21:39

Allah yakara tonamana asirinsu ameeeeen

Antispam
visitors online visitors today visitors yesterday visitors total