XtGem Forum catalog
Aika + f p _ x
WASU SHAFUKAN NTAHAUSA
HOTONA LABARAI
MusicsVideosForumGames ApplicationsThemes
+Labarai Da Rahotonni

Dubu Dari Biyar Aka Ba Mu Domin Mu Kashe Sheik Sani Yahaya Jingir, Inji Maharan Jos Da Zaria

imageimage
Maharan da suka kitsa Harin Bom a Jos da
Zaria sun ce naira dubu dari biyar aka ba su
domin kashe Shugaban Majalisar Malamai
na Kuniyar Izala na Kasa Sheik Malam Sani
Yahaya Jingir.

Sun bayyana haka ne jim kadan bayan
kama su da Rundunar Sojojin kasar an ta yi
jiya a Gombe.

"Ali yana cikin Dajin Sambisa shine ya ce mu
je mu kashe Yahaya Jingir kuma ya ba mu
kudi Naira Dubu Dari Biyar , amma
Abubakar shine ya san komai a cikinmu
mun je da Bom da kuma bindiga amma mai
bindigar ya mutu" inji daya daga cikin
Maharan.

Shi kuwa direban na su ya ce bai san komai
ba, shi dai an ba shi dubu goma aka ce ya
kai su Jos da Zaria idan suka kammala
abinda za su yi ya dawo da su ya sauke su
a inda ya dauke su, wato kan hanyar shiga
MaiDuguri.

Saidai daya daga cikin maharan ya karyarta
Direban na su, inda ya ce babu abunda bai
sani ba domin tare suke aiwatar da komai
da shi.

Shugaban nasu mai suna Abubukar bai
samu damar furta komai ba kasancewa
Raunin dake Kafarsa dalilin harbin Bindiga
ya hanashi cewa
komai.

Rundunar Sojojin Nijeriya dai sun kama
maharan ne a jiya tare da hadin gwuiwar
jami'an tsaro na farin kaya SSS a garin Deba
karamar Hukumar Yamaltu dake Jihar
Gombe a daidai wani shingen binciken
ababen hawa.

Share Button

Mungude da karanta Dubu Dari Biyar Aka Ba Mu Domin Mu Kashe Sheik Sani Yahaya Jingir, Inji Maharan Jos Da Zaria
An wallafa shi a 2015-07-09 18:14
Alaka Maharan Jos Da Zaria , Sheik Sani Yahaya Jingir
Ra'ayuyi Dubu Dari Biyar Aka Ba Mu Domin Mu Kashe Sheik Sani Yahaya Jingir, Inji Maharan Jos Da Zaria
No Photo
Abubakar Haliru Bunza
2015-07-11 22:34

Allah yakara tona asirnsu.

No Photo
Kabiru soja ishaq mohammad
2015-07-11 01:22

Ubangiji yabamu nasara akanku yahudawan qarshan zamani?

No Photo
Abdullahi lawan
2015-07-10 22:33

Allah kasa mudace, Allah yatona asirinsu

No Photo
alaramma
2015-07-10 07:46

Allah mungodema .

No Photo
Anas Yakubu Akuyam
2015-07-10 06:45

Ubangiji Allah {s.w.a} mun godema, da kafara tona asirin dun wanda keda hannu ko sanaiya akan wannan kashe kashen bayin Allah da akeyi a kasar mu Nigeria.

No Photo
Aliyu AA Investmen Nig ltd
2015-07-10 06:19

Alhamdulillah Allah duk wanda yakeda hannu awannan al'amari Allah yatuna asirinsa

No Photo
abubakar Umar hadejia
2015-07-10 06:05

To allah ya kyauta ya karemu daga dukan sharri masau albarka wannan wata da muke ciki

No Photo
Zaharraddeen
2015-07-10 03:59

Allah tonamuku asiri duk indasu ke

No Photo
Bello senior
2015-07-10 03:37

To Allah ya kara Tona asirin azzalumai a duk Inda suke

No Photo
Aminu garba sallau
2015-07-10 02:13

Sojoji ku rikesu sosoi ku tatsi bayanai. Allah ya kara tona musu asiri ameen

Antispam
visitors online visitors today visitors yesterday visitors total