Ring ring
Aika + f p _ x
WASU SHAFUKAN NTAHAUSA
HOTONA LABARAI
MusicsVideosForumGames ApplicationsThemes
+Labarai Da Rahotonni

'Yan kunar bakin wake sun kashe mutani 14 a maiduguri

image
Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ce wasu
mata 'yan harin kurnar bakin-wake su hudu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne sun tayar da bam da ke jikinsu daya bayan
daya a unguwar Sajeri da ke birnin Maiduguri a ranar Alhamis.


Wata sanarwar da kakakin rundunar, Kanal Sani Kukasheka Usman ya aikewa NTA ta ce
uku daga cikin 'yan ta'addan sun tayar da bam dinsu ne a unguwa daya, yayin da ta hudu ta tayar da nata a gaban wani masallaci.

Kanal Usman ya ce ya zuwa yanzu mutane akalla 14 ne suka rasa rayukansu -- ciki har da 'yan kurnar-bakin-waken yayin da
mutane 39 suka jikkata.

Ya yi kira ga mutane -- musamman wadanda ke zama a wuraren da lamarin ya faru --da
su kwantar da hankalinsu kuma su ci gaba da sa ido kan abubuwan da ke wakana a kewayensu, yana mai cewa soji suna yin duk abin da kamata domin tabbatar musu da tsaro.

Sanarwar ta ce abu ne mai muhimanci a tabbatawar wa al'ummar yankin da cewa duk da kokarin da mayakan kungiyar Boko Haram suke yi wajen mayar da hannu agogo baya a ci gaban da ake samu wajen dawo da zaman lafiya da kuma tsaro a cikin kasar, ba za su yi nasara ba.

Share Button

Mungude da karanta 'Yan kunar bakin wake sun kashe mutani 14 a maiduguri
An wallafa shi a 2015-10-02 11:22
Alaka 'Yan kunar bakin wake , Maiduguri
Ra'ayuyi 'Yan kunar bakin wake sun kashe mutani 14 a maiduguri
No Photo
Aliyu Ibrahim Ramalan
2015-10-02 21:45

Allah ya kiyaye, Amin

Antispam
visitors online visitors today visitors yesterday visitors total