Aika + f p _ x
WASU SHAFUKAN NTAHAUSA
HOTONA LABARAI
MusicsVideosForumGames ApplicationsThemes
+Labarai Da Rahotonni

Buhari Ya Aiko Da Sunayen Ministoci Daga Amurka

image
A shirin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake na ganin ya ciki alkawarin da ya dauka na bayyana sunayen ministocinsa kafin karshen watan nan, a jiya Litinin ya mika sunayen ministocin ga mai ba shi shawara ta musamman kan harkokin majalisar dattijai, Sanata ita Enang.

Majiyarmu wadda ke cikin tawagar da suka raka shugaban kasan zuwa Amurka taron majalisar dinkin duniya, ta bayyana cewa Sanata Ita, wanda aka baiwa jadawalin sunayen ministocin ya baro filin jirgin sama
na J.F Kennedy da ke Amurka a daren jiya domin ya gabatar da sunayen ga majalisar dattijai kafin wa'adin da shugaban kasan ya
dauka na bayyana sunayen ya cika.

Majiyar ta kuma kara da cewa Buhari, wanda har zuwa yanzu yana New York wajen taron majalisar dinkin duniyan, ya tattauna da shugaban majalisar dattijai Sanata Bukola Saraki kan lamarin, inda ya kara masa da cewa ya aiko Sanata Ita Enang
domin ya gabatar musu da sunayen wadanda za a baiwa mukaman ministocin a yau ko kuma gobe.

Haka kuma bincike ya nuna cewa takardar na dauke da sunayen mutane 36 da za a baiwa mukaman ministan sabanin jawabin da ya fito a baya na cewa Buhari zai nada ministoci 16 kacal, domin rage yawansu.

Share Button

Mungude da karanta Buhari Ya Aiko Da Sunayen Ministoci Daga Amurka
An wallafa shi a 2015-09-29 03:50
Alaka Amurka , Buhari , Ministoci
Ra'ayuyi Buhari Ya Aiko Da Sunayen Ministoci Daga Amurka
No Photo
Kabir lawal alfataa
2015-10-07 07:45

Allah yabasu juriyar rukon amanar da aka doramasu.

Photo
sadeeqwep
2015-09-29 23:51

<img src="http://ichef-1.bbci.co.uk/news/ws/320/amz/worldservice/live/assets/images/2015/06/10/150610100046bukolasaraki512x288reuters.jpg"/> ALLAH YABASU IKON YIN ADALCI

No Photo
Yusuf khalid
2015-09-29 12:58

Ya allah kabasu ikon yimana adalci da kuma aiki tukuru

No Photo
Abdul,aziz Turakin Nasarawa Saminak
2015-09-29 05:09

Allah Yasamudache

No Photo
Jamilu babale dan faggo
2015-09-29 04:34

ALLAH Yamana jagora. Daga jamilu babale daga garin warri delta state.

Antispam
visitors online visitors today visitors yesterday visitors total

Snack's 1967