XtGem Forum catalog
Aika + f p _ x
WASU SHAFUKAN NTAHAUSA
HOTONA LABARAI
MusicsVideosForumGames ApplicationsThemes
+Labarai Da Rahotonni

DSS takai karar Sambo Dasuki a kotu

image
A Nigeria, hukumar tsaro ta farin kaya DSS
ta ce ta kai karar tsohon mai bai wa shugaban kasar shawara a kan tsaron Kanar Sambo Dasuki mai ritaya a gaban kotu bisa zargin sa da mallakar bindigogi ba bisa ka'ida ba.


A watan Yuli ne hukumar DSS ta kai samame a lokaci guda, a gidaje uku na Sambo Dasukin a Abuja da kuma Sakkwato, inda
daga bisa hukumar ta ba da sanarwar cewa ta gano wasu manyan makamai da motocin
sulke da ka iya yin barazana ga tsaron kasa.

Kanar Sambo Dasuki mai ritaya ya rasa mukaminsa ne bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya sauke manyan hafsoshin tsaron kasar da ya gada daga gwamnatin shugaba Jonathan.

Daga bisani an maye gurbin su da wasu a kokarin da shugaban kasar ya ce yana yi na magance hare haren ta'addanci daga kungiyar Boko Haram.

Share Button

Mungude da karanta DSS takai karar Sambo Dasuki a kotu
An wallafa shi a 2015-09-26 12:31
Alaka A kotu , Dasuki , DSS , Sambo
Ra'ayuyi DSS takai karar Sambo Dasuki a kotu
No Photo
Sani Yakubu
2015-09-26 12:36

Allah Yakaremu

Antispam
visitors online visitors today visitors yesterday visitors total