Aika + f p _ x
WASU SHAFUKAN NTAHAUSA
HOTONA LABARAI
MusicsVideosForumGames ApplicationsThemes
+Labarai Da Rahotonni

Mutane Nagari Da Zurfin Tunani Ne Kawai Zan Baiwa Mukamin Minista, - Buhari

image
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya
bayyana a yau Litinin a babban birnin tarayya Abuja cewa mutane nagari da zurfin tunani ne kawai zai nada a mukaman minista a gwamnatinsa.

Shugaban ya bayyana hakan ne a hirar da gidan talabijin na NTA suka yi da shi a safiyar jiya littinin, inda kuma ya kara da cewa zai
gabatar da sunayen ministocin nan ba da jimawa ba.

“A iya nazarin da na yi muna bukatar ‘yan kasa nagari masu kaifin basira da tunani da ya kamata a ba su mukaman minista.

“Da yawa daga cikin ma’aikatun Nijeiya sun tabarbare, kowa kansa ya sani, wanda kuma hakan ba adalci ba ne. Muna da mutane
masu ilmi da fasaha da kaifin tunani, amma kowa yana kokarin kare kansa ne, inda kawai a tunaninsa nawa zai iya samu cikin
lokaci kankani.

Don haka akwai bukatar a nemi wadanda suka dace domin a ba su
matayin”, inji shugaban kasan.

Share Button

Mungude da karanta Mutane Nagari Da Zurfin Tunani Ne Kawai Zan Baiwa Mukamin Minista, - Buhari
An wallafa shi a 2015-07-27 17:34
Ra'ayuyi Mutane Nagari Da Zurfin Tunani Ne Kawai Zan Baiwa Mukamin Minista, - Buhari
No Photo
Malam.Abdulwahid wasagu kebbi state
2018-07-09 12:45

Munanan muna taya ka da addu,a allah yayi muna jagora amenn thummah ameenn.

No Photo
DANJIMMAI M WALDA
2017-02-23 04:43

fata nagari lamiri ALLAH yaba baba buhari lfy ameeeeeeen

No Photo
Nafiu Sani Kuka Kogo
2017-02-11 02:19

Allah Ya Taimakawa Mai Girma Shugaba Buhari.

No Photo
Maina a maina
2015-08-13 08:36

Wanan yayi dai dai

No Photo
Nura Abubakar Ya'u Dambatta.
2015-08-05 10:41

Wannan yayi daidai Allah yattabbatar masa da nufinsa ameen, muna mika godiyarmu ga Allah (s.w.t) dayakawomu wannan lokaci nayiwa kasarmu garambawul.

Antispam
visitors online visitors today visitors yesterday visitors total

The Soda Pop