XtGem Forum catalog
Aika + f p _ x
WASU SHAFUKAN NTAHAUSA
HOTONA LABARAI
MusicsVideosForumGames ApplicationsThemes
+Labarai Da Rahotonni

Yadda Aka So Halaka Ni Ta Hanyar Yi Min Allurar Guba A Kurkuku. - Obasanjo

image
* Ya Kuma Bayyana Yadda Aka Kashe Janar 'Yar'Adua A Kurkuku.

Tsohon shugaban kasa Janar Olusegun Obasanjo ya bayyana yadda gwamnatin tsohon shugaban kasa na mulkin soja,
marigayi Janar Sani Abacha ta so halaka shi ta hanyar yi masa allura, amma Allah ya kare shi.

Ya kuma bayyana yadda aka kashe amininsa marigayi Janar Shehu Musa 'Yar'Adua a kurkukun garin Fatakwat.

Obasanjo shi da mataimakin nasa Janar 'Yar'Adua a zamanin mulkin soja, suna daga cikn wadanda aka kai su kotun sojoji bisa zargin su da shirya yi wa gwamnatin Abacha juyin mulki.

Kamar yadda Obasanjo ya ce, ya yi shekaru biyar a gidan yari na garin Jos, kafin daga bisani aka sauya shi zuwa gidan yarin garin
Yola, amma a ranar da za a canza shi zuwa Yola, an nemi da ya gana da likita, wanda aka turo domin ya kashe shi cikin ruwan sanyi ta hanyar yi masa allura, amma sai
Allah ya kubutar da shi daga tarkon da aka dana masa.

Tsohon shugaban kasan ya bayyana hakan ne a littafin da ya wallafa mai taken "MY WATCH', inda ya yi waiwayen yadda aka
kama shi aka tsare shi da kuma yadda ya kubuta daga kisan da aka so yi masa.

Obasanjo ya kara da cewa akwai wani likita da aka turo domin ya gwada lafiyarsa, inda likitan ya gaya masa cewa gwamntin Abacha ta damu da lafiyarsa, don haka ne aka turo shi ya duba lafiyarsa, amma sai jikinsa ya ba
shi cewa akwai wata manufa a lamarin, domin cutar da aka ce yana dauke da ita babu a jikinsa.

Don haka ne ya bayyana wa
likitan cewa babu wani gwajin jini da za a yi masa, shi dai ya san cewa yana fama da ciwon suga ne kawai, kuma bai yi tsanani ba.

"Da fadawa likitan haka sai ya maida allurarsa cikin jaka, ya kuma nuna bacin ransa kan kin amincewar da na yi.

Daga baya ne kuma sai na gane cewa shi ma Shehu Musa 'Yar'Adua an yi masa yadda aka yi min, wanda a dalilin haka aka yi masa
allurar da ta yi sanadin mutuwarsa".

Obasanjo ya kara da cewa bayan an sauya masa sheka zuwa gidan yarin Yola, sai aka gabatar masa da wani likita mai suna Dakta
Ajunwo, wanda dan asalin jihar Oyo ne, wanda kuma ya kasance mai duba lafiyarsa har zuwa lokacin da aka sako shi, inda daga
bisani ya maida shi likitinsa bayan ya zama shugaban kasa.

Bayan wasu 'yan makonni kuma, sai ga wani likita mai suna Dakta Yakasai ya sake zuwa daga Abuja domin duba lafiyata, amma na ki amincea na ce ya bari sai likitana Dakta Ajunwo ya zo.

Inda bayan ya zo sai yake tambayar likitan da ya zo daga Abuja cewa me yake bukata, inda bayan ya gaya masa, sai likitan nawa ya debi jinina da kayan aikinsa, ya baiwa likitan".

Likitan nawa ya tambayi takwaran nasa yaushe zai aiko mana da sakamakon, sai ya ce cikin kwanakin biyu bayan ya isa Abuja.

Na ci gaba da zama a gidan yarin na Yola har tsawon shekaru biyu bayan zuwan likitan, kuma babu wani sakamakon jinin nawa da aka aikowa da lkitan nawa.

Babu shakka ya zo da muguwar manufa ne, amma Allah ya sake kare ni".

"Ba a jima da zuwa daukar jinin nawa ba ne, labarin rasuwar Shehu Musa 'Yar'Adua ya zo min.

An yi ta yada jita jitar cewa guba aka ba shi. Domin kamar yadda ni ma likita ya zo gwada jini na da farko, haka shi ma 'Yar'Adua aka yi masa, inda aka yi amfani da wannan gwajin jinin aka yi masa allura mai guba.

Share Button

Mungude da karanta Yadda Aka So Halaka Ni Ta Hanyar Yi Min Allurar Guba A Kurkuku. - Obasanjo
An wallafa shi a 2015-07-27 17:15
Ra'ayuyi Yadda Aka So Halaka Ni Ta Hanyar Yi Min Allurar Guba A Kurkuku. - Obasanjo
No Photo
Yusuf A Yakubu
2016-06-03 00:36

To Allah katsaremu shikuma shehu yar'aduwa Allah kaimasa Rahama

Antispam
visitors online visitors today visitors yesterday visitors total