Pair of Vintage Old School Fru
Aika + f p _ x
WASU SHAFUKAN NTAHAUSA
HOTONA LABARAI
MusicsVideosForumGames ApplicationsThemes
+Labarai Da Rahotonni

Acikin kudaden da Ramalan Yero yace ya bari kusan duka ba kudin da zamu iya amfani dasu bane kai tsaye - El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai yace dole gwamnatinsa ta dinga Sara tana duban bakin gatari domin babu isassun kudaden da zata tafiyar da gwamnati yadda ya kamata.

Ya musanta korafin da tsohon mataimaki gwamnan jihar Nuhu Bajoga yayi cewa wai gwamnatinsu sun bar kudi a asusun gwamnatin cewa babu kanshin gaskiya akan hakan.

Yace nan bada dadewa ba zai bayyana wa mutanen jihar irin sharholiyan da akayi da kudaden jihan da kuma matsayin asusun jihan.

"Da zaran an gama tantance yawan ma'aikatan jihan da akeyi yanzu zamu fede muku birin daga kai har wutsiya" Kakakin gwamnan Samaila Aruwan daya sanya hannu akan wannan jawabi yace gwamnan atsaye yake wajen ganin komai ya wadata a jihar.

Menene zakuce akan hakan?
Share Button

Mungude da karanta Acikin kudaden da Ramalan Yero yace ya bari kusan duka ba kudin da zamu iya amfani dasu bane kai tsaye - El-Rufai
An wallafa shi a 2015-07-06 07:29
Alaka El-Rufai , Ramalan Yero
Zama farkun fadin ra'ayi akan wannan labarin Acikin kudaden da Ramalan Yero yace ya bari kusan duka ba kudin da zamu iya amfani dasu bane kai tsaye - El-Rufai
Antispam
visitors online visitors today visitors yesterday visitors total